Masu ruwa da tsaki za su sake duba Tsare-tsare da Ayyukan aikin Hajjin 2023.
Daga Abubakar Baba Ahmad.
Masu ruwa da tsaki a harkokin Hajji za su hallara a Abuja domin duba Tsare-tsare, shirye-shirye da yadda ake gudanar da ayyukan Hajji da Umrah a kasar nan.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Komitin Yan Jarida na aikin hajji ta kasa IHR, Ibrahim Mohammed ya rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce wannan bitar wani bangare ne na bikin bayar da laccoci da bayar da kyaututtuka na shekara-shekara na IHR wanda aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga Satumba, 2023 a dakin taro na babban masallacin kasa dake Abuja.
Ta ce taron wanda zai gudana tsakanin karfe 10 na safe zuwa karfe 1 na rana zai samu halartan tsohon karamin ministan harkokin waje, Ambasada Zubairu Dada a matsayin shugaban taron.
Sanarwar ta ce, laccar ta bana za ta yi tsokaci ne kan manufofin aikin Hajji da Umrah da tasirinta wajen samun nasarar gudanar da ayyukan Hajji, inda Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Alhaji Zikirullah Kunle Hassan zai kasance babban mai masaukin baki.
“IHR kuma za ta karrama cibiyoyin Hajji, jami’ai da masu gudanar da yawon bude ido da suka yi fice a harkar aikin hajji duk a lokacin aikin hajjin 2023. Irin wadannan ayyuka sun hada da ingantaccen ilimi da wayar da kan maniyyata da kuma hidimtawa ga alhazai a lokacin aikin Hajjin bana,” in ji sanarwar.
Ta kuma bayyana cewa wani gogaggen dan jarida, malami kuma shugaba daga Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, Farfesa Ismaila Shehu zai gabatar da laccar kan manufofin da ake da su a kan harkokin gudanar da aikin Hajji hadi da ayyukan jami’ai da kuma yadda suke da tasiri ga ayyukan Hajji.
A cewar Jami’in na IHR, taron zai kuma bayar da karramawa ta musamman ga wasu gwamnonin da suka yi wa hukumomin kula da jin dadin Alhazai na Jihohinsu tare da ba da lambar yabo ta Gwamnan da yayi fice wajen kula da gudanar da aikin Hajjin bana.